in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambia ta yi kira ga kasasehen Afrika su girmama batun kawar da makamai
2018-02-28 10:12:01 cri

wakiliyar kasar Zambia ta din din din a Tarayyar Afrika AU wato Susan Sikaneta, ta ce lokaci ya yi, da dukkan kasashe mambobin AU za su nuna jajircewarsu, ta hanyar aiwatar da shirin Tarayyar dake da nufin kawar da makamai kawo shekarar 2020.

Susan Sikaneta wadda ta bayyana haka yayin da take ganawa da shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat, da sauran mambobin kwamitin sulhu na Tarayyar jiya Talata a kasar Habasha, ta ce abun takaici ne yadda ake samun yaduwar makamai a galibin kasashen Afrika, bayan kuma shekarar 2018 shekara ce ta kawar da makamai kamar yadda AU ta ayyana.

Ta ce, ya kamata kasashe su jajirce ta hanyar kaddamar da gagarumin shiri na kwace makamai dake zaman barazana ga tsaro da kwanciyar hankalin nahiyar, tana mai kira da a ci gaba da wayar da kan al'umma daga nan har zuwa watan Satumba da Tarayyar ta ayyana a matsayin watan afuwa domin mikawa tare da ajiye makamai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China