in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin Beijing da Tianjin da Hebei na samun ci gaba tare
2018-02-27 10:54:28 cri

A cikin shekaru 4 da suka gabata, sana'o'in dake wurare uku, wato birnin Beijing da Tianjin da kuma lardin Hebei wadanda suke makwabtaka da juna, sun samu kyautatuwa bisa wani shirin da aka tsara. Bayan an dauki jerin manufofin samar da wasu muhimman kayayyakin yau da kullum, yayin da ake hanzarta kafa dandalin hadin gwiwa kan wasu muhimman abubuwa tsakanin wuraren uku. A yanzu, tattalin arzikin yankunan da suka hada da biranen Beijing da Tianjin da kuma lardin Hebei, ya samu tagomashi sosai.

Kokarin fitar da wasu ayyukan da bai kamata su kasance a Beijing, wato babban birnin kasar Sin ba, shi ne aiki mafi muhimmanci a cikin manufar bunkasa birnin Beijing da na Tianjin da kuma lardin Hebei cikin hadin gwiwa. A cikin shekaru 4 da suka gabata, an rufe da kuma fitar da wasu masana'antu wajen dubu 2 da kuma kasuwanni dari 6 daga birnin Beijing, sannan an fitar da wasu makarantu da asibitoci zuwa birnin Tianjin da lardin Hebei.

A idon wasu 'yan kasuwa wadanda suka koma lardin Hebei bayan sun bar Beijing, yawan kudin hayar shago da yawan kudin sayen kayayyakin da suke sayarwa sun ragu, amma yawan sabbin baki 'yan kasuwa ya karu. Sakamakon haka, yawan kudin da suke samu bai ragu ko kadan ba.

Mr. Li Guoyong wanda ya taba sayar da kayayyaki a wata kasuwar dake cikin garin birnin Beijing, da yanzu shi da matarsa ke hayar wani shago a wata kasuwar dake birnin Cangzhou na lardin Hebei, ya shaidawa wakilinmu cewa, "A lokacin da muke kasuwar dake cikin garin birnin Beijing, yawan kudin cinikayya da mukan samu ya kai wajen RMB dubu 10 a kowace rana. Idan muka ware kudin kwadago da na hayar shago da dakin adana kaya da kuma kudin jigilar kayayyaki da muka kashe, yawan ribar da muke samu na kaiwa wajen kashi 10 cikin dari. Yanzu a wannan kasuwa, yawan kudin cinikayya da muke samu kowace rana ya kai wajen RMB dubu 4, amma saboda ba mu bukatar biyan kudin hayar daki da sauran kudade, ribar da muke samu ya na kaiwa wajen kashi 25 cikin dari."

A cikin wani filin yin aikin walda na masana'antar kamfanin Hyundai na Beijing dake birnin Cangzhou na lardin Hebei, na'urorin mutum mutumi wato Robot kusan dari 3 na aikin jigilar kayayyaki da walda kamar yadda ake fata. Yanzu, wannan masana'anta na iya fitar da kananan motoci dubu dari 3 kowace shekara.

Mr. Lang Jiawei, mataimakin babban direktan kamfanin Hyundai na Beijing ya bayyana cewa, kamfaninsa ya gaza fadada girmansa a birnin Beijing saboda rashin isashen fili, sannan yawan kudin da ake amfani da su kan kwadago da jigilar kayayyaki ya yi yawa. Dalilin ke nan da ya sanya kamfaninsa zabar birnin Cangzhou dake lardin Hebei, inda ya gina sabuwar masana'anta, kuma kamfaninsa na cike da imani ga makomar yankin Beijing da Tianjin da Hebei. Mr. Lang yana mai cewa, "Kasarmu tana da wasu yankunan dake samar da motoci, wato yankin delta na kogin Yangtze, da yankin delta na kogin Zhujiang, har ma a yankin arewa maso gabas. Yanzu yankin Beijing da Tianjin da lardin Hebei yana bayansu wajen bunkasa sana'o'i masu alaka da mota. Saboda haka, a ganina, yankin yana da kyakkyawar makoma a nan gaba."

A hakika dai, kamar yadda Mr. Lang ya fadi, yanzu an riga an kafa wani rukunin da ya shafi kera motoci, har ma yawan kudin da aka samu daga rukunin ya kai fiye da RMB biliyan dari.

Sannan a birnin Tianjin, bayan kaddamar da cibiyar hadawa da kuma mika jirgin sama samfurin Airbus A330 a watan Satumban shekarar bara, birnin ya zama cibiyar hada kananan jiragen sama da ma manya kirar Airbus, a wata kasa da ba ta nahiyar Turai ba. Mr. Yang Lin, direktan cibiyar nuna goyon bayan sana'o'in hada jiragen sama ta Tianjin ya bayyana cewa, "Kawo yanzu, an riga an shigar da wasu muhimman ayyukan dake shafar jiragen sama a cibiyar. Bisa hasashen da aka yi, ya zuwa shekarar 2020, tattalin arzikin cibiyarmu da ya shafi hada jiragen sama zai kara samun kyautatuwa, yawan kudin da za a samu zai wuce RMB yuan biliyan 100. Sakamakon haka, birnin Tianjin zai zama daya daga cikin muhimman sansanonin bunkasa sana'o'in jiragen sama a kasar Sin."

Wani abin da ya kamata a ambato shi ne, a watan Afrilun shekarar 2017, an kafa sabon yankin Xiong'an a lardin Hebei, inda ake shigar da wasu sana'o'in zamani daga birnin Beijing da na Tianjin.

Kawo yanzu, birnin Beijing na kokarin bunkasa tattalin arzikin da ya shafi bangarorin fasahohin zamani da sha'anin hada hadar kudi da na samar da bayanai. A shekarar 2017, yawan gudummawar da wadannan sana'o'in suka bayar ga tattalin arzikin birnin Beijing ya wuce kashi 50 cikin dari. A birnin Tianjin ma, ana samun saurin bunkasar sana'o'in kere-kere na zamani da samar da hidima bisa fasahohin zamani. Sannan a lardin Hebei, ana hanzarta kyautata tattalin arziki. Sakamakon haka, a cikin shekaru 4 da suka gabata, tattalin arzikin wadannan yankuna uku suna samun ci gaba bisa shirin da aka tsara. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China