in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar wasannin Kenya ta yi wa dokokinta gyaran fuska domin magance matsalar amfani da magungunan kara kuzari
2018-02-26 10:49:07 cri

Hukumar kula da harkokin wasanni ta kasar Kenya, ta umarci dukkanin kungiyoyin wasannin da ke neman zama karkashinta, da su mika dukkanin dokokinsu na yaki da shan kwayoyi kara kuzari.

Yayin taron majalisar kula da harkokin wasanni ta kasar Kenya na shekara-shekara da ya gudana a ranar Asabar a birnin Nairobi, hukumar koli ta majalisar mai ba da shawarwari ga gwamnati, ta tilastawa dukkanin kungiyoyin wasanni sanya hannu kan daftarin hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta duniya WADA da takwararta ta kasar Kenya domin sanya dukannin kungiyoyin wasanni aiwatar da dokar.

Kasar Kenya ta zage damtse wajen yaki da matsalar shan kwayoyin kara kuzari, wanda ya sa hukumar WADA sanya kasar dake gabashin Afrika cikin jerin wadanda ta ke sanyawa ido a shekarar 2016, saboda gazawarta ta aiwatar da tsauraran dokokin yaki da shan kwayoyin kara kuzari. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China