Bukatar, an mika ta ne ga zaunannen kwamitin wakilan jama'ar kasar Sin, kuma an gabatar da ita bisa ga sabon tsarin gurguzu wanda ya dace da halayyar musamman ta kasar Sin a sabon karni.
Kwamitin tsakiyar ya gabatar da bukatar yin gyaran fuska ga kuduri dokar nan wanda ta nuna "Wa'adin shugaban kasa da mataimakinsa a kasar Sin daidai yake da majalisar wakilan jama'ar kasa, kuma ba za su shafe sama da wa'adin mulki biyu ba" zuwa "Wa'adin shugaban kasa da mataimakinsa a tsarin shugabancin kasar Sin iri daya ne da na majalisar wakilan jama'ar kasa."
Kwamitin tsakiyar na jam'iyyar ta CPC ya mika bukatar sanya kwamishinoni masu gafaka a matsayin wani sabon bangare cikin kundin tsarin mulkin kasar.
A cewar bukatar, za'a sanya kwamishinoni masu gafakar cikin jerin sunayen jami'an gudanar da mulki, da jami'an shari'a, a matsayin wani bangare na shugabancin kasa, dukkansu majalisar wakilan jama'a ne za su samar da su da kuma duba alhakin dake wuyansu da yadda aikinsu ke gudana. (Ahmad Fagam)