An tsara gabatar da zagaye na gabata na shirin abincin Sinawan a cikin shirin girke girke na RTV mai take Foodtube.
An dai nuna shirin abincin sinawan ne a ofishin jakadancin kasar Sin dake Kigali, babban birnin kasar Rwandan.
Jakadan kasar Sin a Rwanda Rao Hongwei, ya bayyana muhimmancin dake tattare da shirin girke girken sinawan, inda yace hakan zai kara bayyana al'adun sinawa da kuma dalilan da suka sanya abincin sinawa ke kara samun karbuwa a duk fadin duniya.
Tao Yukun, mai yin girki a ofishin jakadancin kasar Sin, ya dafa nau'ikan abincin sinawa masu yawan gaske domin nunawa a cikin shirin.
Munyangeyo, wani mazaunin kasar Rwandan ya bayyana cewa, masu kallon shirin talabijin na RTV ne suka bukaci a gabatar musu da shiri kan nau'ikan abincin sinawa. Akwai shagunan dake sayar da abincin sinawa masu yawa a Kigali, kuma mutane suna son a koyar dasu yadda ake girka abincin sinawan domin suma su dafa a gidajensu, in ji shi.(Ahmad Fagam)