in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana yin kwaskwarima ga kamfanonin dake karkashin mallakin gwamnatin kasar Sin
2018-02-23 11:01:45 cri

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, ana gudanar da kwaskwarima kan manyan kamfanonin dake karkashin mallakin gwamnatin kasar Sin, wato an fara shigo da jarin da 'yan kasuwa suka zuba a cikin kamfanonin, ya zuwa karshen shekarar 2017 da ta wuce, adadin kamfanonin da suka aiwatar da irin wannan gaurayen tsari ya zarta kashi 2 bisa 3 a fadin kasar ta Sin.

A halin da ake ciki yanzu, ana yin kwaskwarima kan tsarin gudanar da harkokin manyan kamfanonin dake karkashin mallakin gwamnatin kasar Sin, haka kuma ana hanzartar aiwatar da aikin domin samun sakamako mai gamsarwa, bisa alkaluman da aka samu, an ce, a shekarar 2017 data gabata, adadin manyan kamfanonin dake karkashin mallakin gwamnatin kasar wadanda suka shigo da jarin da 'yan kasuwa suka zuba ya kai 700, kana adadin jarin da suka shigo dasu daga wajen 'yan kasuwa ya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 338 da miliyan 600.

Kamfanin narka karafa mafi girma na kasar Sin wato rukunin narke karfe na Baowu na kasar Sin ya fi nuna fifiko a fannin, kawo yanzu, kananan kamfanonin dake karkashin jagorancin rukunin da yawansu ya kai 115 suna aiwatar da gaurayen tsarin gudanar da harkokinsu wato sun shigo da jarin da 'yan kasuwa suka zuba a ciki, adadin da ya kai kaso 23 bisa dari, haka kuma adadin ribar da rukunin ya samu da yawansu ya kai kaso 70 bisa dari ya zo ne daga wadannan kananan kamfanonin.

Mataimakin babban manajan rukunin narka karafa na Baowu na kasar Sin Hu Wangming ya yi mana bayani cewa, bayan kwaskwarimar da aka yi, karfin gogayya na rukuninsa ya kara karfafuwa bisa babban mataki, ya ce, "Alal misali, a kamfanin ciniki na Ouyeel dake karkashin jagorancin rukunin Baowu na kasar Sin, wasu kamfanoni 6 sun zuba jari a ciki, ma'aikatan kamfanin da yawansu ya kai 126 su ma sun zuba jari a ciki bisa mataki na farko, bisa dalilin gaurayen jarin da aka zuba, kamfanin ya samu cigaba cikin sauri, a shekarar 2017, adadin karafun da kamfanin ya sayar ta yanar gizo ya kai tan miliyan 68 da dubu 350, adadin shine mafi yawa a fannin a fadin kasar ta Sin."

A bara kuwa, rukunin Baowu shi ma ya kafa asusun yin kwaskwarima kan tsarin sana'ar narka karafa na kasar Sin na farko tare da kamfanin WL Ross na kasar Amurka da asusun tsimin makamashi na kasashen Sin da Amurka da rukunin ciniki na CMG, kowanensu ya mallaki hannun jari kusan kaso 25 bisa dari, kwamitin yanke shawara kan zuba jari zai tsai da kuduri kan harkokin asusun bisa sauyawar kasuwa, mataimakin babban manajan rukunin narka karafa na Baowu Hu Wangming ya fayyace cewa, "Daukacin kananan kamfanonin dake karkashin jagorancin rukunin Baowu suna bude kofa ga 'yan kasuwa, ana sa ran za a kara zuba jari cikin rukunin."

Rukunin Chengtong na kasar Sin wato CCT shi ma ya samu babban sakamako yayin da yake gudanar da kwaskwarima kan tsarinsa, kawo yanzu dukiyar rukunin kaso 82.7 bisa dari ta kasance takardun hada-hadar kudi, kana rukunin ya shigo da jarin da babban kamfanin jigilar kayayyaki na GLP ya zuba, adadin jarin da kamfanin ya zuba a rukunin CCT ya kai kaso 15 bisa dari, mataimakin shugaban rukunin CCT Li Yousheng ya bayyana cewa, "Mun shigo da jari daga kasashen waje, mun yi amfani da hanyoyin gudanar da harkokin kamfani irin na zamani daga wajensu, da haka rukuninmu ya samu ci gaba cikin sauri a kasuwar cikin gida na kasar Sin, tare kuma da samun cigaba cikin sauri a kasuwannin kasa da kasa."

An ce, a shekarar bana da muke ciki, gwamnatin kasar Sin za ta sa kaimi kan kwaskwarima kan tsarin gudanar da sana'o'in samar da wutar lantarki da man fetur da iskar gas da layin dogo da jirga-jirgar jiragen saman jigilar fasinjoji da sadarwa da masana'antun aikin soja da sauransu, 'yan kasuwa na kasar Sin da na kasashen waje suna iya zuba jari a ciki, kwararren dake aiki a cibiyar yin nazari kan kamfanonin kasar Sin Li Jin ya bayyana cewa, "A halin da ake ciki yanzu, ana kara zurfafa kwakwarima kan tsarin manyan kamfaninin dake karkashin mallakar gwamnatin kasar Sin, kana an fi mai da hankali kan ribar da za a samu da kuma ingancin tattalin arziki yayin da ake gudanar da aikin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China