Daga cikin kasashen duniya 180, Rwanda ta samu matsayi na 48 cikin kasashen dake da karancin aikata rashawa a duniya, inda ta samu cigaba daga matsayin kasa ta 50 a shekarar 2016, kamar yadda rahoton da aka fitar a Kigali babban birnin kasar ta Rwandanya tabbatar. Ita ma kasar Tanzania ta tashi daga matsayin kasa ta 106 a shekarar 2016 inda ta koma kasa ta 103 a shekarar 2017, a cewar rahoton.
Uganda ta cigaba da rike matsayinta na kasa ta 151 a shekarar 2016, yayin da kasar Burundi ta samu hawa matsayi na 157 bayan ta dan samu cigaba a bangarori biyu idan aka kwatanta da shekarun baya.
Kenya kuwa ta sauka kasa da maki biyu inda ta hau matsayi na kasa ta 143.
Botswana ce kasa ta farko a nahiyar Africa, inda ta samu matsayi na 34 a duniya baki daya, yayin da Seychelles a Afrika ta samu matsayi na 36 a duniya, kamar yadda rahoton ya nuna.(Ahmad Fagam)