Ursula Mueller ta yi kiran ne jiya a birnin Bangui, bayan kammala ziyarar yini 4 da ta kai kasar.
Ta ce Jamhuriyar Afrika ta tsakiya na fuskantar matsalar jin kai, tana mai cewa rikici na ci gaba da yaduwa a kasar, yayin da jama'a ke cikin tsananin bukatar taimako.
Ta kara da cewa fararen hula ne ke ci gaba da fama da radadin rikicin da rashin tsaro.
Rikici tsakanin musulmi 'yan tawayen Seleka da na Anti-Balaka da galibinsu kiristoci ne, ya jefa kasar cikin yakin basasa tun daga shekarar 2013.
Ofishin MDD mai kula da harkokin jin kai ya bayyana kasar a matsayin mai rauni, wadda rikici ya daidaita, kuma take fuskantar kalubalen tattalin arziki da tsare-tsare. (Fa'iza Mustapha)