Shugaban kungiyar Gwamnonin Jam'iyyar APC, Rochas Okorocha ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya a Abuja fadar mulkin kasar.
Da farko dai, Gwamnonin sun halarci taron majalisar zartarwa da ya gudana a fadar shugaban kasar karkashin jagorancin Shugaba Muhammdu Buhari.
Wasu majiyoyi daga jam'iyyar sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, makasudin shirya taron shi ne, shawo kan shugaba Buhari game da bukatar ya sake tsayawa takara a shekarar 2019.
Taron na iya zama dori akan wanda aka yi a garin Daura ranar Juma'ar da ta gabata a gidan Shugaban kasar.
Sai dai kafin haka, Gwamnan dai ya ce manufarsu ita ce yi wa shugaban ta'aziyya game da rashin da ya yi na 'yan uwansa biyu. (Fa'iza Mustapha)