Muhammadu Buhari ya bukaci Ministocin da suka hada da na tsaron kasar Mansur Dan Ali da na harkokin waje Geoffrey Onyeama da kuma Ministan yada labarai Lai Mohammed, su ziyarci kauyen Dapchi na jihar Yobe dake arewa maso gabashin kasar, domin tattaro bayanai na ainihi game da harin da aka kai kwalejin fasaha ta 'yan mata mallakar Gwamnati.
A cewar ministan yada labarai na kasar Lai Mohammed, Shugaba Buhari ya kuma umarci sojoji da sauran hukumin tsaro su karbe ragamar kula da kwalejin tare da ceto 'yan matan da suka bata. (Fa'iza Mustapha)