in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar bunkasa ilimin addinin musulunci ta bukaci a kare yara a yankunan dake fama da rikici
2018-02-22 10:42:14 cri
Hukumar bunkasa ilimin addinin musulunci, kimiyya da raya al'adu,ta bukaci a kara kaimi wajen tabbatar da kare yara a yankunan dake fama da rikici.

Darakta Janar na hukumar Abdulaziz Othman Altwaijri, ya bayyana haka ne yayin taro karo na 5, na ministocin kula da harkokin yara na kasashe mambobin hukumar da aka kaddamar a jiya Laraba.

A cewar Abdulaziz Altawaijri, ta'azarar wahalhalun yara a wurare irin Syria da Yemen da Somali da Libya da Afghanistan, na bukatar shirin dauki na hadin gwiwa.

Ya kuma yi ikirarin cewa, ana ci gaba da take hakkokin da hukumomin duniya suka amince da su na yaran Falasdinu, ta hanyar mamayar yankunan Falasdinun da Isra'ila ta yi.

Darakta Janar din ya kuma yi kira ga kasashen musulmi, su dauki ingantattun hanyoyin magance rikici da musgunawa da cin zarafi da wariyar da ake nunawa yara, tare da samar da tsaro da ingantaccen kiwon lafiya da sauran muhimman abubuwan da yara ke bukata, ya na mai bayyana na su a matsayin halatattun hakkoki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China