in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Rwanda za ta gudanar da bincike kan zanga-zangar da aka yi a sansanin 'yan gudun hijirar Congo
2018-02-22 10:02:14 cri
Gwamnatin Rwanda ta ce rundunar 'yan sandan kasar za ta gudanar da bincike kan musababbin zanga-zangar da aka yi a sansanin 'yan gudun hijira na Kiziba dake lardin Karongi na yammacin kasar, wanda ya kasance matsuguni ga dubban 'yan gudun hijirar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Da yake ganawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Daraktan sashen kula da harkokin 'yan gudun hijira na ma'aikatar tunkarar iftila'i da kula da 'yan gudun hijira ta Rwanda Jean Claude Rwahama, ya ce 'yan gudun hijira da dama sun ji rauni yayin zanga-zangar, inda suka yi ta jifan jami'an tsaro da duwatsu.

Jean Rwahama ya kara da cewa, 'yan gudun hijirar sun kuma yi yunkurin farwa ofishin babban jami'in kula da 'yan gudun hijira na MDD dake Karongi.

Wata sanarwa daga ofishin kakakin Gwamnatin kasar ta ruwaito cewa, Zanga-zangar ta biyo bayan matakin da shirin samar da abincin na duniya WFP ya dauka, na rage tallafin abinci da yake ba dukkan 'yan gudun hijira da Rwanda ke ba mafaka da kaso 25, saboda karancin kudi.

A cewar Jean Rwahama, wakilan 'yan gudun hijira na ganawa da hukumomin sansanin da na yankin tare da sauran hukumomi abokan huldar MDD, inda suke tattaunawa game da lamarin. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China