Tun da farko, dalibai 94 ne aka lura sun bata, bayan hukumomin sun gudanar da kidaya a Kwalejin fasaha ta 'yan mata dake yankin Dapchi na jihar Yobe.
Gwamnatin jihar ta ce 'yan mata 8 sun koma a ranar Talata, sannan wasu 20 ma sun koma da safiyar ranar Laraba, bayan sun tsere daga harabar makarantar saboda farmakin da mayakan Boko Haram suka kai musu.
A cewar Kwamishinan ilimi na jihar Mohammed Lamin, Gwamnati na da yakinin sauran 'yan matan za su dawo nan bada dadewa ba.
A nasa bangaren, Kwamishinan 'yan sandan jihar Abdulmalik Sunmonu ya yi watsi da fargabar da ake ko kungiyar Boko Haram ce ta sace 'yan matan, ya na mai cewa rundunar ba za ta iya cewa akwai batun sace 'yan mata yayin harin na ranar Litinin ba.
A cewarsa, ya tambayi shugabar makarantar ko akwai batun sacewa ko kashe wata daliba, sai dai ta amsa da a'a.
A nasa bangaren, wani malamin makarantar ya ce mayakan Boko Haram sun kutsa dakunan kwanan dalibai, al'amarin da ya sanya 'yan matan tsallake katanga inda suka tsere cikin daji. (Fa'iza Mustapha)