in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abbas ya bukaci kasashen duniya su amince da kasar Palasdinu
2018-02-21 11:35:08 cri

Shugaba Palasdinawa Mahmoud Abbas ya yi kira ga kwamitin sulhun MDD da ya kira taron kasa da kasa wanda zai kai ga amincewa da kasar Palasdinu bisa yarjejeniyar kan iyaka ta shekarar 1967 da aka shata.

Shugaba Abbas ya ce, alummar Palasdinu na kira ga kwamitin sulhun MDD da ya gaggauta kiran taron kasa da kasa a tsakiyar wannan shekara, kamar yadda dokokin kasa da kasa da kudurorin MDD suka tanada. Sannan a gayyaci duk kasashen duniya da bangarorin da abin ya shafa gami dama masu ruwa da tsaki a yankin da ma kasashen duniya. Ya kamata sakamakon taron ya amince da kasar Palasdinu a matsayin cikakkiyar mambar MDD.

Bugu da kari, shugaban Palasdinun ya bayyana fatansa cewa, taron zai kai ga amincewa da kasashen biyu wato Isra'ila da Palasdinu bisa tsarin kan iyakar shekarar 1967 da aka shata.

Daga karshe, Abbas ya yi kira da a bullo da wani managarcin tsari da zai taimaka wajen sasanta bangarorin biyu kan yadda za a kawo karshen batun matsayin Palasdinu kamar yadda hakan ke kunshe cikin yarjejeniyar Oslo.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China