Jama'a assalam alaikum! Yanzu ga wata muhimmiyar sanarwa. Tun daga ranar 1 ga watan Maris din bana, da karfe tara na safiyar kowace rana, agogon Najeriya da Nijar da ma sauran kasashen yammacin Afirka, sashin Hausa na CRI ya fara gabatar muku wasu labarai da dumi-duminsu kai-tsaye, ta kafar shafin sada zumunta na Facebook, wato CRI HAUSA.