in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Gambiya ya bukaci 'yan kasar su rungumi zaman lafiya da kaunar juna
2018-02-19 12:49:48 cri

Shugaban kasar Gambiya, Adama Barrow, ya bukaci jama'ar kasar da su rungumi kaunar juna da yin hakuri da juna don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Barrow, ya shedawa daruruwan jama'ar kasar a birnin Banjul, a lokacin bikin cika shekaru 53 da samun 'yancin kan kasar, ya ce kasar za ta cigaba da samun kwanciyar hankali da lumana ne kadai idan al'ummarta suka rungumi dabi'ar kaunar juna, kuma da zarar 'yan kasar suka sadaukar da kansu don baiwa kasar gudunmowa, ta haka ne Gambiya za ta zama wata mashahuriyar kasa.

Ya ce, "A ko da yaushe muna da bambance-bambance a tsakaninmu amma dole ne sai mun koyi da halayyar girmama juna da kaucewa nuna bambanci a tsakanin juna."

Ya ce, dole ne al'ummar Gambiya su sani cewa duk da irin bambance bambancen siyasa, da kabila, da tattalin arziki, da bambancin jinsi dake tsakanin juna, amma abin da ya kamata a sani shi ne dukkan mu 'yan kasar Gambiya ne, in ji Barrow.

Barrow ya ce, "Mun kawo karshen yaki da mulkin kama-karya, wannan shi ne bangare mafi sauki. Tabbatar da zaman lafiya da samun demokaradiyya shi ne babban kalubalen dake gabanmu."

"Wannan yana bukatar hakuri, yarda da juna, kuma za'a iya samun wasu kura-kurai, amma za mu iya gyara su idan har muka yi aiki tukuru don samar da sabuwar kasar Gambiya".(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China