in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres: Rediyo da wasanni za su taimakawa jama'a cimma burinsu
2018-02-14 10:39:56 cri

Jiyar Talata, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, radiyo wani babban makami ne, kana kafar sadarwa mai araha dake sada mutane da dama a sassa daban-daban na duniya, baya ga yadda wannan kafa ke sada al'ummomi da harkokin wasannin dake faruwa a yankunan karkara.

Sakataren wanda ya bayyana hakan albarkacin ranar rediyo ta duniya, ya ce rediyo zai kuma hada kan al'umma da kuma samarwa musu kafar dogaro da kai, da baiwa wanda ba a jin duriyarsu damar bayyana ra'ayinsu. Ya kuma bayyana cewa, an tsara rediyo ne ta yadda zai kai ga al'ummomin dake yankunan masu wahalar shiga da wadanda ke cikin wani hali, kamar wadanda ba su iya karatu da rubutu ba, da nakasassu da matalauta.

Ya kara da cewa, rediyo yana kuma samar da wata kafa ta shiga muhawarar bainar jama'a, ba tare da la'akari da matsayin karatu ko ilimin jama'a ba, baya ga rawa ta musamman da yake takawa wajen isar da sakonnin gaggawa da agazawa wadanda bala'i ya rutsa da su.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China