in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin Afirka sun yi kira da a yi amfani da ilimin sararin samaniya don bunkasa tsaro da raya kasa
2018-02-14 10:27:10 cri

Ministocin ilimi da masana fasahar sadarwa ta zamani daga kasashen Afirka, sun yi kira da a yi amfani da ilimin sararin samaniya wajen zakulo matakan kawo karshen manyan kalubalen dake addabar nahiyar, kamar kangin talauci da rikice-rikice da cututtuka da kuma matsalar sauyin yanayi.

Jami'an sun yi wannan kira ne yayin taron masana kan harkokin sararin samaniya na kasa da kasa da aka shirya a birnin Nairobin kasar Kenya, dandalin da ya zayyana rawar da kimiyyar sararin samaniya zai taka wajen farfado da rayuwar al'ummomin dake nahiyar.

A jawabinta na bude taron, sakatariyar tsaro a fadar shugaban kasar Kenya Raychelle Omamo ta ce hanya guda ta magance kabulalen tattalin arziki da jin dadin jama'a, da lafiya da muhalli da nahiyar ke fuskanta, ita ce farfado da bangaren sararin samaniya.

Omamo ta bayyana cewa, kasar Kenya ta koyi managartan matakan da kasashen Afirka ta kudu da Najeriya da Aljeriya da Sudan suka dauka a fannin kimiyyar sararin samaniya wajen bunkasa sashen nazarin sararin samaniyarta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China