Moghalu ya shaidawa manema labarai a birnin Legas, cibiyar kasuwancin kasar cewa, lokaci ya yi da masana da kwararru za su karbi ragamar kasar daga hannun 'yan siyasa.
Tsohon ma'aikacin bankin ya ce, ya kamata a raba batun siyasa da kabilanci a Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka ta yadda za ta bunkasa ta kuma koma kan matsayinta na jagora a nahiyar.
Ya ce, yadda manyan jam'iyyun siyasun kasar ke rarraba madafun iko tsakanin shiyoyin kasar a baya ba lallai ne a yi amfani da wannan tsari a wannan lokaci ba. Kamata ya yi a halin yanzu a yi amfani da cancanta maimakon kabila ko yankin da mutum ya fito.
Da ya juya ga batun wa'adi na biyu da shugaba Muhammadu Buhari ke nema, Moghalu ya ce, kundin tsarin mulkin ya baiwa shugaban 'yancin neman sake tsayawa takara.
Ya kara da cewa, wajibi ne Najeriya ta sake tunani game da karfafa wanzuwar sassa masu zaman kansu maimakon ci gaba da dagora kan man fetur.(Ibrahim)