in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 66 a biranen kasar cikin shekaru biyar
2018-02-12 11:15:22 cri

Ministan kula da ma'aikata da tsaron jama'a na kasar Sin Yin Weimin ya bayyana cewa, kasarsa ta samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 66 a biranen kasar cikin shekaru biyar din da suka gabata.

Alkaluman hukuma na nuna cewa, a cikin shekaru 5 din da suka gabata sama kaso 90 cikin 100 na daliban da suka kammala karatunsu a kwalejojin kasar sun samu ayyukan yi, kana an sake daukar sama da ma'aikata miliyan 1.1 dake zaman kashe wando sakamakon rage yawan kayayyakin da masana'antun kasar ke samarwa fiye da kima.

Bayanai na cewa, ya zuwa karshen shekarar 2017 da ta gabata, adadin marasa aikin yi a biranen kasar ya kai kaso 3.9 cikin 100, adadi mafi kankanta tun shekarar 2002.

Sai dai daga shekarar 2013 zuwa 2017, an samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 13 a biranen kasar a ko wace shekara, duk da matsalar da aka fuskanta sakamakon tasirin shirin nan na yiwa tattalin arziki kwaskwarima da koma bayan ci gabansa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China