in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kara karfafa nazarin aikin bincike a fannin kimiyya a kasar Sin
2018-02-12 10:51:41 cri

Kwanan baya gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takarda game da yadda za a kara inganta yadda ake gudanar da harkokin bincike a fannin kimiyya a kasar.

Jiya Lahadi wani jami'in ma'aikatar kula da kimiyya da fasaha ta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, duk da cewa, kasar ta Sin ta samu nasarori wajen bincike a fannin kimiyya, amma har yanzu akwai wasu matsaloli, a don haka kasar Sin take kokari matuka domin kara karfafa ayyukan kirkire-kirkire, ta yadda za a cimma burin gina babbar cibiyar kimiyya da babu kamarta a duniya a nan kasar Sin nan da shekarar 2050.

Aikin bincike a fannin kimiyya yana da muhimmanci matuka yayin da ake yin nazarin kimiyya, game da sakamakon da aka samu a fannin a nan kasar Sin a cikin 'yan shekarun da suka gabata kuwa, shugaban hukumar kula da aikin bincike a fannin kimiyya ta ma'aikatar kula da kimiyya da fasaha ta kasar Sin Ye Yujiang ya fayyace a yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya cewa, "A ko wace shekara, hukumar nazarin bayanan kimiyya da fasaha ta ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta yi nazari kan rahotannin da aka fitar game da bincike a fannin kimiyya, kuma alkaluma na nuna cewa, adadin rahotannin kimiyya da aka wallafa a nan kasar Sin ya kai matsayi na biyu a fadin duniya a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kana adadin abubuwan da aka rubuta a cikin rahotannin wadanda sauran ma'aikatan kimiyya suka yi amfani da su shi ma ya kai matsayi na biyu. A fili yake cewa, kasar Sin ta kasance a sahun gaba a fannin nazarin kimiyya, misali a watan Janairun bana, an yi nasarar tagwaita halittar wasu jan biri guda biyu nau'in macaques (Makak), inda aka yi amfani da matakan kimiyya wajen tagwaita tinkiyar Dolly, sakamakon da ya yi muhimmin tasiri a fannin nazarin kimiyya a fadin duniya."

A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ta fito da wani cikakken tsarin gudanar da aikin bincike a fannin kimiyya, har ta samu ci gaba cikin sauri, duk da haka, an fuskanci wasu matsaloli yayin da ake kokarin nazarin kimiyya, misali karancin babban sakamakon kimiyya wanda zai yi babban tasiri ga rayuwar jama'a da karancin masu aikin bincike a fannin kimiyya da karancin kudin da ake bukata yayin da ake aikin da sauransu.

A cikin takardar da gwamnatin kasar Sin ta fitar kwanan baya, an tsara shirin aikin da za a yi a nan gaba, shugaban hukumar kula da aikin bincike a fannin kimiyya ta ma'aikatar kula da kimiyya da fasaha ta kasar Sin Ye Yujiang ya bayyana cewa, "Aikin da za a yi a nan gaba ya kunhe fannoni uku, na farko za a fito da tsarin kirkire-kirkire domin taimakawa masu aikin bincike a fannin kimiyya, ta yadda za su gudanar da aikin yadda ya kamata, na biyu za a kara mai da hankali kan aikin bincike a fannin kimiyya, saboda aikin yana da muhimmanci matuka, na uku, za a kara samar da kudaden da ake bukata a wannan fannin, ta yadda za a gudanar da aikin lami lafiya."

Takardar ta nuna cewa, nan da shekarar 2020, matsayin aikin bincike a fannin kimiyya na kasar Sin zai ci gaba sosai, kana tasirin da kasar Sin za ta kawo wa kasashen duniya a fannin zai kara habaka matuka, kana nan da shekarar 2035, kasar Sin za ta shiga sahun gaba a wannan fannin a fadin duniya, ban da haka kuma ana sa ran cewa, nan da shekarar 2050, kasar Sin za ta kasance babbar cibiyar nazarin kimiyya da babu kamarta a duniya.

Game da batun rike amana yayin gudanar da aikin nazarin kimiyya, mataimakin ministan ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Huang Wei ya jaddada cewa, rike amana abu ne mai muhimmanci yayin da ake aikin nazarin kimiyya, ya kara da cewa, yanzu a nan kasar Sin, hukumomin da abin ya shafa sama da 20 sun kafa wata kungiya ta musamman domin kare aukuwar cin amana, Huang Wei yana mai cewa, "Za a kara karfafa aikin hana aukuwar lamarin, idan nan take za a rika gano yadda masu aikin nazarin kimiyya suke gabatar da sakamako na jabu, saboda yadda aka kafa tsarin tattara bayanansu, a sa'i daya kuma, ana kokarin tantance sakamakon da aka gabatar, ta yadda za a yi nasarar hana aukuwarsu."

Jami'in shi ma ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan hadin gwiwa dake tsakaninta da sauran kasashen duniya wajen bincike a fannin kimiyya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China