in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole Iran da Syria su dauki alhakin harin jirgi mai sarrafa kansa, in ji firayin ministan Isra'ila
2018-02-11 12:57:54 cri

A daren jiya Asabar, firayin ministan kasar Isra'ila Banjemin Netanyahu ya sanar da cewa, ya zama wajibi kasashen Iran da Syria su dauki alhakin harin sama da aka kai Isra'ila da jirgin sama mai sarrafa kansa a wannan rana, ya kara da cewa, Isra'ila za ta ci gaba da daukar matakan da suka wajaba domin tabbatar da ikon mallaka da kuma tsaron kasarta.

Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa, a safiyar wannan rana, wani jirgin sama mai sarrafa kansa ya tashi sama daga wani sansanin Syria, daga baya ya shiga yankin dake karkashin mamayar Isra'ilan, inda nan take sojojin Isra'ila suka harbo shi da jirgin sama mai saukar ungulu har ya fadi kasa, bayan haka, sojojin Isra'ilar sun kai hari ta sama a wasu sansanonin aikin soja na kasar Iran da jiragen saman yaki har sau biyu.

Rundunar sojojin Isra'ilan ta kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, Isra'ila ba ta niyyar tsananta lamarin, amma za ta yi martani ga wadanda suka lahanta moriyar kasarta.

Bisa labaran da wasu kafofin watsa labarai suka bayar kan wannan batun, wai an ce Iran din ta kai hari ga Isra'ila da jirgin sama mai sarrafa kansa, sai dai bangaren Iran din ya musanta, kuma ya bayyana cewa, zargin da ake yi masa ba shi da tushe balle makama.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China