in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya aike da sakon taya murnar bikin bazara ga kasar Sin
2018-02-11 12:15:51 cri
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya aikewa gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sinawa sakon taya murnar bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin da kuma bikin bazara a yayin da ake jajiberin fara bukukuwan, kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar.

A cikin wasikar da shugaba Buhari ya aikewa takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, ya yi fatan kara samun kyautatuwar dankon zumunci a cikin sabuwar shekarar domin amfanin al'ummomin kasashen biyu.

"A yayin fara shagulgulan bikin murnar shekarar kare bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, wanda za ta fara daga ranar 16 ga watan nan na Fabrairu, muna taya al'ummar Sinawa samun nasarar gudanar da shagulgulan sabuwar shekarar lami lafiya", in ji sanarwar.

Shugaba Buhari ya ce, a shekarar da ta gabata, kasar Sin ta cimma nasarori masu tarin yawa, musamman ta fuskar bunkasuwar tattalin arziki, da siyasa da huldar diplomasiyya da kasashen duniya.

"Samun nasarar aiwatar da babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 ya bude wani sabon babi ga kasar Sin a sabon karni a matsayinta na wata kasa mai jagorantar duniya ta fuskar ci gaban kirkire-kirkire, da tsaro, da yaki da talauci, da ci gaban kayayyakin more rayuwa, da harkokin kudi", in ji shugaba Buhari.

A makon da ya gabata ne aka gudanar da shagulgulan bikin bazara a Najeriya, inda aka gudanar da bikin nuna al'adun kasashen Sin da Najeriya wanda ya gudana a birnin Abuja, fadar mulkin kasar.

Shugaba Buhari ya yaba da kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Najeriya da kasar Sin, ya ce yana fatan kara kyautata mu'amalar siyasa, tattalin arziki, raya al'adu, da zamantakewa tsakanin kasashen biyu.

Ya ce yana fatan ganin taron koli na dandalin Sin da Afrika wato (FOCAC) wanda za'a gudanar a birnin Beijing a watan Satumbar wannan shekarar, tare da nuna kyakkyawar fatan cewa shekarar kare za'a samu nasarori masu yawa a cikinta, kuma za'a samu nasarar kara kyautatuwar dangantaka tsakanin Sin da Afrika cikin wannan shekarar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China