in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burundi ya yaba wa dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin
2018-02-09 10:45:36 cri

Shekarar 2018, shekara ce ta cika shekaru 55 da kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Burundi. A kwanan baya, shugaba Pierre Nkurunziza ya zanta da manema labarun kasar Sin a Bujumbura, hedkwatar kasar Burundi, inda ya yi wa al'ummar Sinawa fatan alheri bisa murnar zuwan bikin sabuwar shekara ta bazara.

A lokacin da yake ganawa da manema labaru na kasashen waje karo na farko a shekarar 2018, shugaba Pierre Nkurunziza ya zabi zantawa da manema labaru na kafofin yada labaru na kasar Sin a ofishinsa a ran 6 ga watan Faburairu.

A lokacin da yake tabo dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin shekaru 55 da suka gabata, dangantakar hadin gwiwa irin ta sada zumunta tsakanin kasashen biyu, tana dada karfafa. Ya ce a lokacin da kasar Burundi take cikin hali mafi tsanani, kasar Sin ta tsaya mata, kuma ta ba da taimako sosai. A idon al'ummar Burundi, kasar Sin ta wuce wata abokiyar hadin gwiwa kawai. "A kullum, kasar Sin na kokarin taimakawa kasar Burundi a fannonin ba da ilmi, da kiwon lafiya, da kayayyakin more rayuwar al'umma da dai makamatansu. Yanzu haka, kasashen biyu na hadin gwiwa kan wasu muhimman ayyukan more rayuwar al'umma, kamar gina sabuwar fadar shugaban kasarmu. Sannan kasar Sin ta samar wa kasar Burundi dimbin kayayyakin masarufi, kamar shinkafa da kayayyakin gine-gine, kamar siminti. Yanzu kasashen Burundi da Sin na kasancewa abun koyi wajen yin hadin gwiwa. Bangarorin biyu na yin hadin gwiwa irin ta cin moriya tare bisa ka'idar mutunta juna. Kuma a idon kasar Burundi, kasar Sin ta kasance aminiya kuma 'yar uwa."

A 'yan shekarun baya, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka na dinga samun ci gaba kamar yadda ake fata. A shekarar 2018, za a shirya taron kolin dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afirka, FOCAC, inda za a kara tattaunawa kan yadda za a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Bisa gayyatar da aka yi mata, kasar Burundi ma za ta aika wakilinta zuwa wajen taron kolin. Shugaba Nkurunziza ya ce, wannan taron koli yana da muhimmiyar ma'ana ga kokarin kara bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen Afirka da Sin.

"Ina godewa shugaba Xi Jinping bisa gayyatar kasarmu Burundi wajen wannan taron dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afirka. Kasarmu Burundi za ta halarci wannan taron kolin. Dandalin tattaunawa tsakanin kasashen Sin da Afirka wani dandali ne mai kyau, dake bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. A kowane taron dandalin da aka shirya, a kullum kasar Sin na gabatar da wasu shirye-shiryen taimakawa kasashen Afirka, inda kasar Burundi ma ta ci moriyar hakan. Ina fatan za a cimma nasarar shirya wannan taron koli na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afirka a birnin Beijing. Tabbas kasar Burundi za ta yi amfani da wannan taro, domin kara bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasarmu da kasar Sin."

Sannan, a watan jiya, gabannin taron kolin kungiyar tarayyar Afirka wato AU karo na talatin, wata kafar watsa labaran kasar Faransa ta ruwaito wani rahoton dake cewa, wai kasar Sin tana satar bayanai a asirce game da harkokin AU. Game da wannan batu, shugaban Pierre Nkurunziza ya bayyana cewa, gaskiya rahoton ba shi da tushe balle makama, kana, hanya ce kawai da wasu kasashen yammacin duniya suke amfani da ita, domin gurgunta alakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka.

"Ba wannan ne karo na farko da wasu kafofin watsa labaran kasashen yammacin duniya, ke amfani da irin wadannan rahotanni domin kawo cikas tsakanin wasu kasashe ba, da haifar da fitina ko haddasa da kiyayya tsakanin kasashen duniya. Yanzu haka kasar Sin ta zamo babbar aminiyar hadin-gwiwar kasashen Afirka. A ganina, wadannan kafofin watsa labarai ba za su cimma nasara ba, saboda a kullum, kasar Sin da kasashen Afirka na kokarin bunkasa dangantakar dake tsakaninsu bisa ka'idar mutunta juna da cin moriya tare."

Daga karshe dai, shugaba Nkurunziza ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance muhimmiyar abokiya ga kasashen Afirka, wadda kuma ba za'a iya maye gurbinta ba. Ya ce tabbas dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Burundi ma za ta ci gaba da kara samun ci gaba. A gabannin bikin bazara, wato bikin murnar sabuwar shekara na gargajiya bisa kalandar wata ta kasar Sin, shugaba Nkurunziza ya nuna gaisuwa ga al'ummomin Sinawa, inda ya ce, "Ina taya al'ummar Sinawa murnar bikin bazara, ina muku fatan koshin lafiya, da samun nasara a sabuwar shekara." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China