in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shanghai ya kafa kotu mai alaka da laifuka ta intanet
2018-02-09 10:19:08 cri

Gwamnatin birnin Shanghai ta kaddamar da kotun farko ta yin shari'u da suka jibinci masu aikata laifukan dake da nasaba da mu'amala ta shafukan intanet ko kuma damfara a harkokin kasuwanci ta intanet.

A cewar kotun shari'a ta unguwar Changning dake Shanghai, kararrakin da suka shafi kasuwanci ta shafukan intanet za'a iya warware su ne ta yanar gizo.

Kotun wanda aka kafa ta a watan Janairu, kawo yanzu, ta karbi kararraki kimanin 106 da suka shafi laifukan zamba a harkokin cinikayya ta shafukan na intanet.

Tun daga shekarar 2014, kotun gundumar ta warware matsalolin da suka shafi kararraki kan batutuwan intanet sama da 3,300 da aka gabatar mata.

Kasancewar al'ummar Sinawa suna juya akalar harkokinsu na sayen kayayyaki ta shafukan intanet da biyan kudaden ta shafukan, ya zama tilas a kafa kotunan da za su tabbatar da tsaron na'urorin zamani da kuma warware rigingimu da suka shafi mu'amala ta intanet.

Kasar Sin ta kafa kotun intanet ta farko ne a watan Agustan bara a lardin Zhejiang dake gabashin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China