in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tauraron Beidou zai ba da hidima ga sama da kasashe da yankuna 200
2018-02-09 10:10:39 cri
Tsarin ba da hidima na fasahar sadarwa da tauraron dan Adam na Beidou zai samar nan gaba kadan, zai amfani kasashe da yankuna da yawan su ya kai sama da 200 a sassan duniya daban daban.

Ofishin kamfanin NORINCO na kasar Sin ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yana mai cewa a yanzu haka kamfanin "Qianxun Spatial Intelligence Inc", dake ba da hidimomi ta tauraron na Beidou wanda NORINCO da kamfanin Alibaba suka kafa, na samar da hidima ga sama da abokan hulda miliyan 90.

Yayin taron shekara shekara na kamfanin NORINCO, an bayyana cewa fadin hidimar "Qianxun" za ta karade dukkanin sassan babban yankin kasar Sin a shekarar nan ta 2018, a yayin da tauraron na Beidou mai samar da managartan bayanai zai fara ba da hidima ga al'umma a dukkanin sassan rayuwa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China