in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gambiya ta sake shiga kungiyar kasashen renon Ingila
2018-02-09 09:52:00 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Gambiya ta tabbatar da cewa, kasar ta sake shiga kungiyar kasashen renon Ingila wato Commonwealth.

Bisa ga bayanan da aka fitar, an ce kasar ta sake zama mamba ne bayan da shugabannin kasashen mambobin na Commonwealth suka amince da bukatar da kasar Gambiyan ta mika na neman ba ta damar sake zama mamba a kungiyar.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin Gambiya ta lura da tasirin da Commonwealth din ke da shi, musamman wajen ci gaban harkokin gudanarwar gwamnatin Gambiyar, da kuma irin rawar da take takawa wajen bayar da shawarwarin da za su bunkasa ci gaban kasar ta fuskar siyasa, tattalin arziki, da zamantakewar al'umma.

Gwamnatin Gambiyar ta yi amanna cewa, sake zama mamba a kungiyar zai taimaka wa kasar wajen farfado da kimarta a idanun kasashen duniya. Kana ta jaddada aniyarta ta mutunta manufofi da ka'idojin dake kunshe cikin dokokin kungiyar ta Commonwealth.

Sanarwar ta ce, gwamnatin Gambaiyar tana fata zamanta a matsayin mambar zai ba ta damar cin gajiyar raya fannonin tattalin ariki da zamantakewar al'ummarta, musamman ci gaban mata da matasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China