in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin a Rwanda ya jinjinawa alakar kasashen biyu
2018-02-09 09:39:48 cri
Jakadan Sin a kasar Rwanda Rao Hongwei, ya jinjinawa alakar kasar sa da Rwanda, yana mai cewa shekarar 2017 ta shiga kundin tarihin kyakkyawar alakar sassan biyu.

Rao Hongwei wanda ya bayyana hakan jiya Alhamis a birnin Kigali, albarkacin murnar zagayowar sabuwar shekarar gargajiya ta al'ummar Sinawa, ya ce mu'amala tsakanin jami'an kasashen biyu, da ma ci gaban aminci dake tsakanin su, ya nuna ingancin manufar siyasa tsakanin kasashen.

Jamaka Rao Hongwei ya kara da cewa, hadin gwiwa tsakanin Sin da Rwanda, ya kara kyautata a fannoni da dama, ciki hadda na cinikayya, da zuba jari, da kiwon lafiya, da ilimi, da yawon bude ido da musaya tsakanin al'ummun su.

Jakada Rao ya ce a bana, Sin da kasar Rwanda za su kara bunkasa alakar su yadda ya kamata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China