in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta farfado da sufuri ta hanyar damkawa kamfanoni masu zaman kansu
2018-02-09 09:16:17 cri

Ministan sufurin Najeriya Hadi Sirika ya bayyana cewa, gwamnatin kasar tana duba yiwuwar farfado da kamfanin sufurin jiragen sama na Nigeria Airways mallakar gwamnatin kasar, inda za ta damka alhakin tafiyar da shi a hannun kamfanoni masu zaman kansu.

Sirika ya shedawa 'yan jaridu a Legas, cibiyar kasuwancin kasar cewa, ana sa ran za a mika kamfanin ne a wa'adin mulki na farko na shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Ya ce, gwamnatin kasar ta tsame kamfanin sufuri na Lufthansa Consortium dake da sansaninsa a kasar Jamus daga cikin wadanda za su ja ragamar sabon tsarin sufurin Najeriyar.

Ministan ya ce, ana sa ran nan da wasu 'yan watanni masu zuwa, wata guda ko kuma watanni biyu, za'a kafa wannan sabon tsarin sufurin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China