in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta karyata jita-jitar da kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka yada
2018-02-08 20:07:00 cri
Bayan ganawarsa da shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU Moussa Faki a yau Alhamis a birnin Beijing, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya zanta da manema labaru, inda ya karyata jita-jitar da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka yada, wai kasar Sin ta yi amfani da damar gina cibiyar tarurukan kungiyar AU don leken asirin kungiyar.

A cewar ministan na kasar Sin, cibiyar tarurukan kungiyar AU wata alama ce ta zumuncin dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, don haka ba za a yarda a shafa mata kashin kaji ba. Kasar Sin ta ba da tallafin gina cibiyar, yayin da kungiyar AU da kasashen Afirka suke amfana da cibiyar, don haka su ne ke da ikon bayyana yanayin da hadin gwiwar bangarorin 2 yake ciki.

Jami'in ya kara da cewa, huldar dake tsakanin Sin da Afirka ta shiga wani zamani na bunkasa cikin sauri. Amma wasu mutane ba sa son ganin haka. Sai dai bisa la'akari da yanayi mai kyau da ake ciki a fannin hadin gwiwar Sin da Afirka, yunkurinsu na kawo matsala tsakanin sassan biyu, ba zai yi wani tasiri ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China