in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An samu raguwar kudaden gudanarwa a shekarar da ta gabata
2018-02-08 13:41:53 cri
Mahukuntan kasar Sin sun cimma nasarar rage kudaden da ake kashewa a fannin bada hidima ta gudanar da hada hadar kasuwanci a shekarar da ta gabata, a wani mataki na saukaka harkokin cinikayya. Yawan kudaden da suka ragu sakamakon daukar wannan mataki dai sun kai kudin Sin Yuan biliyan 88.16, kwatankwacin dalar Amurka biliyan14.

Da yake bayyana hakan yayin taron karawa juna sani a jiya Laraba, mataimakin ministan sufurin kasar Li Xiaoming, ya ce adadin ya haura wanda aka yi hasashen samu da kaso 13 bisa dari. Mr. Xiaoming ya kara da cewa, an cimma nasarar hakan ne sakamakon rage kudaden harajin hanyoyin mota, da soke kudaden gwajin ababen hawa, da rage kudaden hidimar kamfanonin fito.

Ya ce ma'aikatar sufuri za ta kara daukar matakai na rage kudaden samar da hidimomi sama da na shekarar 2017, yana mai bayyana sassan sufurin kaya ta jiragen kasa, da banbanci a yanayin haraji na hanyoyin mota daban daban, a matsayin dabarun da za a aiwatar.

Duk dai da cewa kudaden samar da hidima sun ragu cikin 'yan shekarun baya bayan nan, har yanzu adadin kudade da ake kashewa a fannin yana da yawan gaske, inda ya samar da kaso 14.9 bisa dari na GDPn kasar a shekarar 2016, adadin da ya haura kaso 8 zuwa 9 bisa dari da mafi yawan kasashen da suka ci gaba ke samu daga fannin.

Gwamnatin Sin dai na daukar karin matakai na rage kudaden da ake kashewa wajen samar da hidima a matsayin mataki na kawo sauyi a fannin samar da hajoji. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China