in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a shirya gasar wasannin Olympics ta matasa ta 2022 a Afirka
2018-02-08 10:13:52 cri

Jiya Laraba 7 ga wata, kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics na kasa da kasa ya sanar da cewa, da yammacin wannan rana aka tsara kudurin cewa, za a shirya gasar wasannin Olympics ta matasa ta yanayin zafi karo na hudu na shekarar 2022 a Afirka. Wannan ne dai karo na farko da za a shirya tgasar wasannin Olympics a nahiyar.

Gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ajin matasa ta yanayin zafi, ita ce irin ta mafi girma da ake gudanarwa a duniya. An kuma kaddamar da tgasar karo na farko ne a shekarar 2010, kana za a shirya karo na uku a birnin Buenos Aires na kasar Argentina a watan Oktoban bana wato shekarar 2018 da muke ciki.

Bisa ka'idar da aka zartas, a yayin taron kwamitin wasannin motsa jikin Olympics na kasashen duniya a shekarar 2016, za a kara kyautata hanyar zabar birnin da zai shirya gasar wasannin Olympics ta matasa karo na hudu a maimakon yin gogayya kawai, haka kuma za a saukaka ayyukan dake da nasaba da zabar birnin, kana za a rage lokacin gudanar da hakan, yayin da kuma za a kammala aikin cikin gajeren lokaci. Ban da haka kuma, ana sa ran cewa, za a samar da karin damammaki ga sauran birane dake fadin duniya domin su shiga wasannin na Olympics.

Shugaban kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics na kasashen duniya Thomas Bach ya bayyana cewa, nahiyar Afirka mahaifa ce ta fitattun 'yan wasannin Olympics, wadanda suka samu babban sakamako, kana daukacin kasashen Afirka suna cike da kuzari, musamman ma wajen wasannin motsa jiki. Wannan shi ma dalili ne da ya sa aka tsai da kudurin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2022 a nahiyar. Nan gaba kuma kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics na kasashen duniya zai tuntubi kwamitocin wasannin Olympics na wasu kasashen Afirka domin tantance batutuwa masu nasaba da hakan; kamar batun ta yaya za a shirya gasar wasannin Olympics ta matasa karo na hudu na shekarar 2022 a kasashen Afirka.

A cikin makonni masu zuwa, kwamitin wasannin Olympics na kasashen duniya zai gudanar da hadin gwiwa tsakaninsa da kwamitocin wasannin Olympics na wasu kasashen Afirka, domin tattaunawa kan yadda za a shirya gasar ta shekarar 2022 a Afirka, kana da ma'aunin da za a yi amfani da shi yayin da ake zabar birnin da zai shirya gasar wanda za a sabunta; Misali ta yadda zai dace da ci gaba, da yin amfani da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a na yanzu, ko a gina wasu cibiyoyin wasannin motsa jiki na wucin gadi idan an samu isassun kudade. Wato abu mafi muhimmanci shi ne a sanya kokari bisa hakikanin yanayin da wurin ke ciki, tare kuma da sa kaimi ga matasan kasashen Afirka, wajen kara nuna kuzari kan wasannin motsa jiki. A karshe dai, kwamitin wasannin motsa jikin kasashen duniya zai sanar da sunan birnin da zai shirya gasar karo na hudu na shekarar 2022, a gun bikin kaddamar da taron karo na uku da za a gudanar a birnin Buenos Aires a watan Oktoban bana.

Wasannin motsa jiki na Olympics suna da dogon tarihi da ya zarta shekaru dari daya, kamar yadda shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasashen duniya Thoms Bach ya bayyana. Ya ce fitattun 'yan wasan kasashen Afirka suna da yawan gaske, amma har yanzu ba a taba shirya gasar wasannin motsa jiki na Olympics a kasashen ba tukuna.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, kwamitin wasannin Olympics na kasashen duniya, suna gudanar da ayyuka da dama domin sa kaimi kan ci gaban wasannin motsa jiki, da zamantakewar al'umma a nahiyar Afirka; Misali an kafa cibiyar raya wasannin Olympics ta matasa a kasar Zambiya, an kuma tsara shirin hada kai a kasashen Afirka da dai sauransu. Ban da haka kuma, kwamitin shi ma ya yi hadin gwiwa tsakaninsa da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, inda suka kafa asusun 'yan gudun hijira na wasannin motsa jikin Olympics a shekarar 2017, wanda zai samar da tallafin kudin gina kayayyakin motsa jiki ga 'yan gudun hijirar wadanda suka rasa muhallansu.

Kan wannan batu, mamban kwamitin wasannin Olympics na kasashen duniya daga kasar Habasha Dagmawit Berhane ya nuna gamsuwarsa, inda ya bayyana cewa, har kullum matasan kasashen Afirka suna fatan fitattun 'yan wasan kasashen duniya za su shiga nahiyar domin kara fahimtar kasashen.

Mamban kwamitin 'dan asalin kasar Morocco, wanda ya taba zama zakarar wasan tsallake shinge yayin taron wasannin Olympics Nawal El Moutawakel shi ma ya bayyana cewa, yana farin ciki matuka da ganin za a shirya taron wasannin Olympics a nahiyar Afirka, inda ba a taba shirya irin wannan gasa ba a tarihi. Ya ce ko shakka babu lamarin zai kawo babban alheri ga kasashen Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China