in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Afirka ta kudu ya zanta da shugaba Zuma game da batun murabus
2018-02-08 10:03:06 cri

Mataimakin shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce ya zanta da shugaban kasar Jacob Zuma, don gane da kiraye kirayen da ake wa Mr. Zuman na ya sauka daga mukamin shugabancin kasar.

Mr. Ramaphosa ya ce, tattaunawar ta su ta yi armashi, ta kuma share fagen daukar matakai na gaba, wadanda za su tallafa wajen kawo karshen wannan turka turka ta siyasa.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba, mataimakin shugaban kasar ya ce, zantawar ta su ta ba su damar kammala nazartar al'amura, da kuma mika rahoto ga sassan da batun ya shafa nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Masu fashin baki da dama dai na ganin kalaman na Ramaphosa ba su fayyace karara matsayar da aka cimma da shugaba Zuma ba.

Shi dai mataimakin shugaban kasar ya ce, shi da Mr. Zuma sun yi amannar al'ummun Afirka ta kudu na matukar bukatar ganin an kawo karshen wannan danbarwa. Ya ce, matakan da suke dauka a yanzu za su samar da babbar damar ganin bayan kalubalen da siyasar kasar ke fuskanta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China