Matsalar sufuri ta kawo illa ga bunkasuwar tattalin arzikin kauyukan kasar Sin, don haka gina hanyoyin mota ya taka muhimmiyar rawa wajen ga kokarin da gwamnati ke yi na kawar da talauci da samun wadata ga manoma. A shekarun baya baya nan, Sin ta yi kokarin gina hanyoyin motoci da nufin saukaka zirga-zirgar ababan hawa a hanyoyin dake kauyukan kasar. (Zainab)