in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a karbi baki masu yawon shakatawa kimanin miliyan 385 a kasar Sin a yayin bikin bazara
2018-02-07 13:08:40 cri

A dab da bikin bazara na Sinawa, a jiya Talata, hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ta bayyana cewa, yawon shakatawa ta riga ta zama wata muhimmiyar hanyar da al'ummar Sinawa ke bi wajen murnar bikin bazara. A yayin bikin na wannan shekara, an yi hasashen yawan baki masu yawon shakatawa da za a karba a nan kasar zai kai kimanin miliyan 385.

Ranar 16 ga wata za a fara bikin gargajiya mafi muhimmanci ga al'ummar Sinawa, wato bikin bazara wanda ke alamanta shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya. A jiya Talata, ofishin kula da harkokin labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira taron manema labarai, inda ta bayyana shagulgulan da za a shirya sabo da bikin da kuma harkokin yawon shakatawa a lokacin bikin.

Mr. Wang Xiaofeng, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ya ce, za a ci gaba da samu bunkasar kasuwannin yawon shakatawa a yayin bikin bazara na wannan shekara. Bisa binciken cibiyar kididdiga ta hukumar ta gudanar, sama da kashi 80% na al'ummar Sinawa suna da niyyar yin yawon shakatawa cikin farkon watannin uku na wannan shekara, kuma rabi daga cikinsu suna son yin yawon ne a lokacin bikin bazara. A hasashen da aka yi, a lokacin bikin, za a karbi baki masu yawon shakatawa kimanin miliyan 385, kuma harkokin yawon shakatawa za su samar da kudin shiga kimanin yuan biliyan 476 ga kasar, adadin da ya karu da kimanin kashi 12% bisa makamancin lokacin bara.

Wang Xiaofeng ya ce, idan an yi la'akari da kasuwannin yawon shakatawa a lokacin bikin bazara, yankin kudu da kuma na arewa za su zama sassan da suka fi samun karbuwa, ya ce, "Wasu za su zabi yankin kudancin kasar ne sabo da yanayi mai dumi a yankin, a yayin da wasu za su zabi sassan arewacin kasar sabo da su shakata da wasannin kankara. A binciken da aka yi, an ce, kashi 65.9% na baki masu yawon shakatawa za su zabi yawon shakatawa mai tsayi da mai matsakaicin zango, kuma biranen Sanya da Haerbin su ne wuraren da masu yawon shakatawa suka fi zaba, wato tsibirin teku da kuma wurin da ake iya wasan kankara sun fi samun farin jini wurin masu yawon shakatawa."

A yayin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri, matsayin Sinawa mazauna kasashen waje ma na dinga daukakawa. Don haka, kasancewar bikin bazara wani muhimmin bikin gargajiyar Sinawa, al'adun da suka shafi bikin ma suna ta kara yaduwa daga kasar Sin zuwa kasashen duniya. Daga bikin bazara na shekarar 2010, sai ma'aikatar al'adu ta kasar Sin da ma sauran sassan kasar suka fara kaddamar da harkokin musanyar al'adu da suka shafi bikin bazara a kasashe daban daban, don murnar bikin bazara tare da kara fahimtar da su a kan al'adun kasar Sin.

A yayin bikin bazara na wannan shekara kuma, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da wannan aiki a birane sama da 400 da ke kasashe da shiyyoyi sama da 130 a fadin duniya, ciki har da kasashe da shiyyoyi sama da 53 da ziri daya da hanya daya suka ratsa. Malam Yang Zhijin, mataimakin ministan al'adu na kasar Sin ya bayyana cewa, za a isar da gaisuwar sabuwar shekara ta Sinawa ga duk duniya ta hanyar shirya wasanni da shagulgulan gargajiya da kuma dandana abincin kasar Sin. Ya ce, "A shekarar 2018, za mu kara hada gwiwa da cibiyar fasaha ta Kennedy da ta Lincoln, da ma sauran mashahuran cibiyoyin fasaha na ketare. Har wa yau, za mu kara kaddamar da shagulgula na fahimtar al'adun kasar Sin a sassan al'ummar kasashen ketare, misali makarantu da unguwanni, don jawo hankalin karin al'umma a kan al'adun kasar Sin."

Malam Yang Zhijin ya kara da cewa, za a kuma bayyana harkokin cinikayya da yawon shakatawa da kuma wasannin motsa jiki a shagulgulan murnar bikin bazara, kuma wasannin Olympics na lokacin hunturu ma za su zama wani abin da ke jawo hankalin al'umma a shagulgulan na wannan shekara.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China