Bayan bikin, shugaban Laberiya, George Weah, ya gana da 'yan sandan kwantar da tarzoma da kasar Sin ta tura zuwa Laberiya karo na biyar, inda ya gode musu saboda babbar gudummawar da suka bayar ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Laberiya. Weah ya kuma dauki hoto tare da 'yan sandan kasar Sin. (Murtala Zhang)