in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta cimma nasarar gwajin na'urar da aka girke a kasa ta kakkabo makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango
2018-02-06 11:08:02 cri
Ofishin watsa labaru na ma'aikatar tsaron kasar Sin ya bayar da labari a yau cewa, jiya ranar Litinin, kasar ta yi wani gwajin na'urar da aka girke a kasa ta kakkabo makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango a cikin yankin kasar, kuma an cimma nasarar gwajin. An bayyana gwajin da cewa na kiyaye tsaro ne, ba shi da nasaba da wasu kasashe.

Bisa labarin da aka bayar an ce, a kafin hakan, kasar Sin ta taba yin irin wannan gwaji na na'urar kasa ta kakkabo makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango a watan Janairu na shekarar 2010, da watan Janairu na shekarar 2013. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China