in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin kyautata muhallin kauyuka a kasar Sin
2018-02-06 10:53:36 cri

A halin da ake ciki yanzu, mahukuntan kasar Sin suna kokarin gina kauyuka masu kyan gani, a don haka jiya Litinin an fitar da wata takardar gwamnati game da yadda za a kyautata muhallin rayuwar manoma dake kauyuka, inda aka gabatar da cewa, nan da shekarar 2020, za a yi kokarin cimma burin kyautata muhallin kauyuka a bayyane.

Ofishin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin sun fitar da wannan takarda ne cikin hadin gwiwa, inda suka bayyana cewa, za su kara da mai da hankali kan aikin kyautata muhallin rayuwar manoma a kauyukan kasar. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, duk da cewa an riga an samu wasu sakamakon a wannan fanni, amma duk da haka akwai rashin daidaito yayin da ake kokarin kyautata muhalin kauyuka; misali a wasu yankunan kasar, manoma suna fama da matsalolin muhallin da bai dace da rayuwarsu ba. A karkashin irin wannan yanayi, an fitar da takardar, musamman ma domin gudanar da aikin kyautata muhallin rayuwar manoma yadda ya kamata.

A cikin takardar, an bayyana cewa, idan ana son cimma burin, ya fi dacewa a kara mai da hankali kan aikin a fannoni uku, wadanda ke kumshe da bola wato abin da aka zubar, da ruwa maras tsabta, da tsarin gine-gine. Shehun malamin dake aiki a cibiyar nazari kan kimiyyar zamantakwar al'ummar kasar Sin Li Guoxiang yana ganin cewa, wadannan batutuwa uku sun fi muhimmanci yayin da ake kokarin kyautata muhallin kauyuka, yana mai cewa, "Bola a kauyukan kasar Sin, har yanzu ba a juya ta yadda ya kamata, a don haka kamata ya yi a kara mai da hankali kan aikin sarrafa bola. Kana game da ruwa maras tsabta a kauyuka, musamman ma ruwan da ake fitarwa bayan da aka yi amfani da shi, har yanzu ba bu tsari na sarrafa shi, shi ya sa ya zama dole a yi amfani da wannan dama; wato karkashin jagoranci da kuma goyon baya na gwamnati, a kyautata muhallin kauyuka a fadin kasar."

A cikin takardar, an fi mai da hankali kan bolar zaman rayuwa na yau da kullum da manoma suke zubarwa, shehun malamin kwalejin koyar da ilmomin kiyaye muhalli ta jami'ar Tsinghua ta kasar Sin Liu Jianguo ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, ban da wasu kauyukan dake yankuna masu ci gaba a kasar Sin, hakika ba a fara sarrafa bola ba, shi ya sa matsalar bola ta kawo babban tasiri ga muhalli, har take haifar da illa ga ruwa da gonaki kai tsaye.

A cikin takardar, an bayyana cewa, ya dace a tsara tsarin sarrafa bola da zai dace da yanayin da kauyukan ke ciki, Liu Jianguo yana mai cewa, "Ina ganin cewa, wannan aiki yana bukatar isassun kudi, domin idan ana son gudanar da aikin yadda ya kamata, dole ne a kashe kudi masu yawa, shi ya sa ina ganin cewa, kudi ya fi muhimmanci. Kana ana bukatar jagorancin kwararrun a fannin, shi ma wannan yana da muhimmanci matuka."

Kasar Sin tana da fadi, kuma akwai bambanci tsakanin yaukana daban daban, a don haka ya kamata a tsara shiri iri iri ga wurare daban daban bisa hakikanin yanayin da suke ciki. An yi hasashe cewa, ya zuwa shekarar 2020, a wasu yankunan kasar Sin, misali, yankunan dake gabashin kasar da tsakiyar kasar da kuma yammacin kasar, muhallin kauyuka zai samu kyautatuwa a bayyane, a sauran yankunan kasar kuwa, za a yi kokarin cimma burin sarrafa bola har kaso 90 bisa dari, kana za a gina bayan daki mai tsabta a kauyukan har su kai kaso 85 bisa dari. Kaza lika, a yankunan dake fama da talauci, za a yi kokarin samar da muhallin rayuwa mai tsabta ga manoma.

Shehun malamin dake aiki a cibiyar nazari kan kimiyyar zamantakwar al'ummar kasar Sin Li Guoxiang ya ba da shawarar sa cewa, ya kamata a kara samar da goyon baya ga kauyukan dake tsakiya da kuma yammancin kasar, yana mai cewa, "Dole ne gwamnatin kasar Sin ta dauki hakkin kyautata muhallin kauyuka, bai kamata ba a gaza wajen kula da wannan aikin a bar manoma su yi kokarin gudanar da hakan su kadai. Har wa yau yana da muhimmanci a kara samar da kudi domin aikin, musamman ma a kauyukan dake tsakiya da yammacin kasar ta Sin."

Takardar dai ta bayyana cewa, za a sa kaimi kan kamfanonin kasar Sin domin su shiga aikin, ta yadda za su taka rawa a ciki tare da gwamnatin kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China