in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zazzabin Lassa ya hallaka mutane 31 a Najeriya
2018-02-06 14:45:55 cri
Ministan ma'aikatar lafiya a tarayyar Najeriya Isaac Adewole, ya ce annobar zazzabin Lassa da ta barke a wasu sassan kasar, ta haddasa rasuwar mutane 31.

Ministan wanda ke wannan tsokaci yayin wani taro na masu ruwa da tsaki a ofishin hukumar kula da cututtukan dake bukatar kulawar gaggawa dake birnin Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce gwaje gwaje da aka gudanar sun nuna cewa cutar ta yadu a jahohin kasar 15, kuma mutane 105 ne suka kamu da ita.

Mr. Adewole ya kara da cewa, a shekarar 2018 din nan kadai, an samu mutane 77 da suka kamu da cutar ta Lassa. Yayin taron game da yaki da cutar, ministan ya bukaci cibiyar binciken harkokin kiwon lafiya ta kasar NIMR, da sauran cibiyoyin bincike da su maida hankali ga binciken yanayin sassauyawar wannan cuta. Ya ce zazzabin Lassa ya fi yaduwa a lokacin bazara, amma a yanzu yana ci gaba da bazuwa a kowane lokaci.

Ana dai iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ne ta hanyar tsaftace muhalli, da kaucewa taba abubuwan da bera ya taba, tare da kyautata tsaftar jiki.

Jihohin da aka samu bullar wannan cuta dai sun hada da Bauchi, da Filato, da Taraba, da Nasarawa, da Benue, da Kogi, da Ebonyi, da Rivers. Sauran sun hada jihohin Imo, da Anambra, da Edo, da Delta, da Ondo, da Osun da kuma Lagos. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China