in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trioka sun yi kira ga kasashen dake makwabtaka da Sudan ta kudu da su kakaba mata takunkumin hana sayar mata da makamai
2018-02-05 20:58:49 cri

Kawancen kasashen yammaci (Troika) wanda ya kunshi kasashen Norway da Amurka da Burtaniya sun yi kira ga kasashen dake makwabtaka da kasar Sudan ta kudu, da su kakaba mata kunkumin hana sayar mata da makamai, a wani mataki na matsawa bangarorin kasar da ba sa ga maciji kan su tsagaida bude wuta a tsakaninsu.

A tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua jakadan Sudan ta kudu dake Habasha James Morgan, ya yi watsi da matakin Amurka na kakabawa kasarsa takunkumin hana sayar mata da makamai. Yana mai cewa, a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta, Sudan ta kudu tana da 'yancin sayan bindigogi don tabbatar da tsaron yankunanta, da amfani da doka da oda a kasar da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'ummarta.

Ya kara da cewa, yanzu haka Sudan ta kudu ba ta sayan makamai daga Amurka kuma hakan ba zai taba yin tasiri kan takunkumin hana sayar mata da makaman da aka kakaba mata ba, kuma Amurka ta kakaba mata wannan takunkumi ne don nuna isa da kuma biyan muradunta.

Troika dai tana cewa, hana shigar makamai kasar zai taimaka wajen kawo karshen wahalar da jama'ar kasar ke fuskanta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China