in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Koriya ta Kudu ta yi maraba ga tawagar wakilan Koriya ta Arewa
2018-02-05 16:17:18 cri
A yau Litinin ne gwamnatin kasar Koriya ta Kudu, ta yi maraba da zuwan tawagar wakilan kasar Koriya ta Arewa, dake karkashin jagorancin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasa ta Koriya ta Arewa Kim Yong Nam, wadda ta kai ziyara a kasar a bisa shirin halartar gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da za a yi a birnin PyeongChang.

Kakakin gwamnatin kasar Koriya ta Kudu Kim Eui-kyeom ya bayyana a yayin taron manema labarai cewa, ya zuwa yanzu, Kim Yong Nam ya kasance babban jami'i na farko cikin dukkanin jami'an Koriya ta Arewa da suka taba ziyartar kasar Koriya ta Kudu.

Hakan dai ya nuna aniyar kasar Koriya ta Arewa wajen kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma kyakyyawan fatan kasar na cimma nasarar gudanar da gasar.

Haka kuma, ya ce, a matsayin kasar da ta shirya gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na wannan karo, kasarsa za ta karbi tawagar wakilan kasar Koriya ta Arewa da hannu biyu-biyu, a sa'i daya kuma, kasar Koriya ta Kudu za ta yi shiri sosai, game da ganawa, da tattaunawar da za a yi a tsakanin jami'an kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China