in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta aiwatar da manyan tsare-tsare na farfado da kauyuka
2018-02-05 11:05:31 cri

A jiya Lahadi ne kasar Sin ta kaddamar da takardar kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar, dake ba da jagoranci kan ayyukan da suka shafi batutuwan kauyuka, da aikin gona da kuma manoma. Wannan takarda ita ce ta 15 da kasar ta kaddamar tun da aka shiga sabon karni, kuma ta kunshi babban shirin kasar Sin na farfado da kauyuka a cikin sabon zamani.

Wannan takardar da kasar Sin ta kaddamar a wannan shekara, mai taken "Ra'ayoyin kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar game da aiwatar da manyan tsare-tsaren farfado da kauyuka", ta ba da shiri a dukkan fannoni da nufin farfado da kauyuka, inda aka bayyana ma'ana, da tabbatar da manufar da za a bi da kuma burin da za a cimma, har ma da gabatar da bukatu a fannin.

A cikin takardar an nuna cewa, an aiwatar da manyan tsare-tsaren na farfado da kauyuka ne, domin biyan bukatun wajabci wajen kawar da sabani, a tsakanin karuwar bukatun jama'a kan zaman rayuwarsu, da rashin daidaito da ke kasancewa wajen samun ci gaba, da kuma tabbatar da ganin an kafa zamantakewar al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni, a yayin da JKS ta cika shekaru 100 da kafu, tare da cimma burin kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani mai wadata, da bin tsarin demokuradiya, da wayin kai da kuma jituwa nan da shekara 2049, wato yayin bikin cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar Jama'ar Sin, kana da nufin tabbatar da samun wadata tare a dukkan al'ummar kasar. Game da haka, shehu malami na kwalejin kimiyyar sha'anin noma na kasar Sin Qin Fu yana ganin cewa,

"Idan an duba muhimman batutuwan da ake ambata cikin takardar, za a ga cewa, da farko an gabatar da nuna fifiko wajen neman ci gaban aikin gona, da harkokin kauyuka, wannan ya nuna cewa, ko da yaushe kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwar kasar na mai da hankali sosai kan batutuwa uku na kauyuka, da aikin gona da kuma manoma. A cikin 'yan shekarun nan, an kaddamar da jerin takardun masu lamba 1 ne bisa wannan tushe."

Baya ga haka, Qin Fu ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta samu wasu nasarori kan raya aikin gona da harkokin kauyuka, amma duk da haka akwai wasu matsaloli, ciki har da rashin ingancin ci gaban aikin gona, da babban gibi a tsakanin manoma da na mazauna a birane wajen kudin shiga. A cikin takardar an jaddada cewa, kawar da matsalolin da ake fuskanta na da amfani ga samun ci gaban birane da kauyuka tare yadda ya kamata, da daidaita dangantakar dake tsakanin birane da kauyuka, da kuma rage gibi a tsakaninsu. Qin Fu ya ce,

"Ta hanyar shiga da gwamnatin ta yi, da kuma daidaita harkokin tattalin arziki daga dukkan fannoni, za a samu amfani a fannin ci gaban aikin gona, da harkokin kauyuka, da manoma a dukkan fannoni, da kuma kara ingancin samun ci gaban, ban da wannan kuma, za a iya neman sabon karfi na ciyar da aikin gona da na kauyuka gaba, da karfafa karfin takararsu."

Wannan takarda mai lamba 1 da aka kaddamar a shekarar bana, ta yi tanaji sosai a fannonin karfafa ingancin ci gaban aikin gona, da inganta bunkasuwar kauyuka ta hanyar kiyaye muhalli, da wadatar da al'adun kauyuka, da kafa sabon tsarin gudanar da harkokin kauyuka, da kuma karfafa matsayin ba da tabbaci ga zaman rayuwar manoma. Ciki kuwa, an kuma mai da hankali kan daukar takamaiman matakai na yaki da talauci. Game da haka, shehu malami Zhang Qi, shugaban sashen nazarin aikin kawar da talauci na jami'ar horar da malamai ta birnin Beijing yana ganin cewa, kafin shekarar 2020, aikin kawar da talauci zai kasance daya daga cikin muhimman ayyukan na manyan tsare-tsaren farfado da kauyuka na kasar. Zhang Qi ya ce,

"Bayan shekarar 2020, mai yiwuwa ne matsalar fama da talauci da wasu mutane ke fuskanta, wadanda yawan kudin shigar su ke kasa da matsakaicin na sauran al'umma za ta kasance babbar matsala da za ta kawo cikas ga farfadowar harkokin kauyuka, amma a yanzu haka, matsalar fama da talauci da wasu mutane ke fuskanta, wadanda kudin shiga da su ba su iya biyan bukatun zaman rayuwarsu, ita ce babbar matsala, kuma kamata ya yi mu yi kokarin kawar da irin wannan talauci. Bayan haka kuma, ya kamata a mai da hankali kan kawar da talauci a yankunan dake fama da talauci ta hanyar tsimin makamashi, da kiyaye muhalli." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China