in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar manyan jami'an Koriya ta Arewa za ta halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu a PyeongChang na Koriya ta Kudu
2018-02-05 10:46:22 cri

Kamfanin dillancin labaru na tsakiya na kasar Koriya ta Arewa ya labarta yau Litinin cewa, tawagar manyan jami'an Koriya ta Arewa za ta ziyarci kasar Koriya ta Kudu, tare da halartar bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da za a yi a watan da ake ciki a birnin PyeongChang.

An labarta cewa, manufar wannan tawagar manyan jami'an Koriya ta Arewa karkashin shugabancin Kim Young-Nam, shugaban zaunannen kwamitin majalisar jama'ar koli ta Koriya ta Arewa ita ce, halartar bikin bude gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu karo na 23.

A ranar 9 ga watan Janairun bana, bayan da manyan jami'an Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu suka yi wata tattaunawa a Panmunjom dake yankin da aka haramta ayyukan soja tsakanin kasashen biyu, sun ba da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka cimma daidaito kan halartar Koriya ta Arewa a gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta PyeongChang, da kuma gudanar da shawarwari tsakanin jami'an sojan kasashen 2.

Koriya ta Arewa ta ce, za ta tura tawagar manyan jami'anta, da tawagar wakilan kwamitin Olympic na kasar zuwa gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta PyeongChang.

Za a gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu karo na 23 daga ranar 9 zuwa 25 ga watan Febrairun bana a birnin PyeongChang na kasar Koriya ta Kudu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China