in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Za a gudanar da gwajin cutar daji na kasa baki daya
2018-02-05 10:00:37 cri

Ministan ma'aikatar lafiya na tarayyar Najeriya Isaac Adewole, ya ce an kammala dukkanin shirye shirye, na fara gudanar da gwajin cutar daji ko Cancer a dukkanin fadin kasar.

Isaac Adewole ya ce, za a yi gwajin ne kan nau'o'in cutar daji da suka fi addabar al'ummar kasar, wato cutar daji ta mama da ta mahaifa ga mata, sai kuma cutar daji ta mafitsara dake addabar maza.

Ministan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar, albarkacin ranar cutar daji ta duniya wadda a bana aka yiwa lakabi da "Za mu iya, zan iya."

Adewole ya ce, akwai bukatar al'umma su rika lura da alamun farko na kamuwa da cutar, duba da cewa gano alamun ta da wuri, na ba da damar shawo kan ta ko magance illar ta.

Daga nan sai ya ja hankalin al'ummar Najeriya da su yi watsi da duk wasu canfi, ko daukar matakai na tsangwamar masu dauke da cutar ta daji.

Kwararru a fannin kiwon lafiya dai na ganin cewa, sai an yi hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da al'umma, za a kai ga magance yawaitar masu kamuwa da cutar daji a duniya.

Ranar Lahadi 4 ga watan nan ce ranar cutar daji ta duniya, an kuma yi amfani da ranar ta bana, wajen tattauna hanyoyin bankado dabarun dakile ci gaban wannan cuta, da rage radadin tasirin ta ga al'ummar duniya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China