in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
India ta nemi taimakon Najeriya da Benin don gano jirgin ruwanta da ya salwanta
2018-02-04 12:34:24 cri
India ta nemi taimakon kasashen Najeriya da jamhuriyar Benin domin gano jirgin ruwanta wanda ya bace a tekun yammacin Afrika kimanin sa'o'i 48 da suka shude, inda kasar ke fargabar ko an sace jirgin ruwan ne.

Shi dai jirgin ruwan mallakar wani kamfanin Indiya ne dake Mumbai, yana dauke ne da man gas wanda adadin kudinsa ya kai kusan dalar Amurka miliyan 8 da kuma matukan jirgin ruwan 'yan kasar ta Indiya su 22.

Indiya ta nemi taimakon dakarun tsaron teku na kasashen Najeriya da Benin domin gano jirgin ruwan wanda ya yi batan dabo.

Mahukuntan Indiya sun ce, tuni hukumar kula da fito da ruwan kasar ta tuntubi takwarorinta na kasashen Najeriya da jamhuriyar Benin domin su taimaka wajen gano jirgin ruwan.

Jami'an Indiyan sun ce har zuwa yanzu babu wani labari game da jirgin ruwan.

Ko a watan Janairu ma, sai da wani jirgin ruwa ya bace a tekun jamhuriyar Benin, kwanaki biyu daga bisani aka samu labarin cewa an yi fashin jirgin ruwan ne. (Ahamd Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China