Zhang Dejiang ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin na maida hankali sosai kan habaka alakar hadin-gwiwa, da karfafa dankon zumunci tare da kasashen Afirka. Sin na fatan Mauritius za ta ci gaba da yin amfani da dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, gami da shawarar ziri daya da hanya daya, domin sa kaimi ga ci gaban huldodinta da kasar Sin, da samar da alfanu ga jama'arsu.
A nasa bangaren Shanti Bai Hanoomanjee ya bayyana cewa, Sin aminiyar arziki ce ta Mauritius, kuma Mauritius na tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duk fadin duniya. Kana majalisar dokokin kasar za ta fadada hadin-gwiwa da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, don sanya sabon kuzari ga ci gaban dangantakar kasashensu.(Murtala Zhang)