in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa ya zargin Amurka da yunkurin ruguza sulhu tsakaninta da Koriya ta Kudu
2018-02-02 13:27:51 cri
Wasu rahotanni na cewa, a ranar 31 ga watan Janairun da ya shude, ministan harkokin wajen kasar Koriya ta Arewa Ri Yong Ho, ya aike da wata wasika ga babban magatakardan MDD, inda ya zargi kasar Amurka da yunkurin rushe shirin sulhu a tsakanin kasarsa da kasar Koriya ta Kudu, yana mai kira ga MDD da ta mai da hankali kan wannan batu, tare da daukar matakan da za su dace don warware matsalar.

Haka kuma, an ce, babban jirgin ruwa mai dauke da jiragen sama samfurin "Carl Vinson" zai isa yankin tekun dake kusa da zirin Koriya a ranar 9 ga watan nan da muke ciki, wato kafin bude gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta yanayin sanyi a birnin Pyeongchang. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China