in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda ta yi bikin tunawa da ranar 'yan mazan jiya
2018-02-02 11:51:31 cri

A jiya Alhamis kasar Rwanda ta shirya bikin tunawa da ranar 'yan mazan jiya a duk fadin kasar, kana an ziyarci makwancin jarumar kasar da suka kwanta dama don girmama su.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, da manyan shugabannin gwamnatin kasar da jami'an diplomasiyya sun halarci bikin, inda suka bi sahun iyalan 'yan mazan jiyan kasar don ziyartar makwancinsu dake Remera, a Kigali babban birnin kasar.

Baya ga ainihin bikin da aka gudanar a hukumance, an kuma gudanar da bukukuwan a dukkan lunguna da sako na kasar, inda al'ummar kasar ta Rwanda suka taru a wuri guda don girmamawa da nuna yabo ga irin gudummawar da 'yan mazan jiyan suka baiwa kasar.

Bikin na ranar Alhamis ya kunshi gangamin wayar da kan al'umma na tsawon mako guda dangane da nuna kyakkyawar sadaukarwar da 'yan mazan jiyan suka nuna, inda aka dinga yin kiraye kiraye ga 'yan kasar musamman matasa, da su rungumi manufofi 4 na kasar Rwandan, da suka hada da hadin kan kasa, aiki tukuru, nuna kishin kasa, da jajurcewa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China