in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara tafiye-tafiyen bikin bazara na shekarar 2018
2018-02-02 11:05:39 cri

Jiya Alhamis 1 ga watan fabrairu ne, Sinawa a nan kasar Sin suka fara tafiye-tafiyen bikin bazara na wannan shekarar da muke ciki, hakan ya alamanta cewa, an fara gudanar da aikin jigilar fasinjoji kimanin biliyan 3 a kasar.

An yi hasashe cewa, yawan fasinjojin da za su yi zirga-zirga a wannan lokacin zai kai kimanin biliyan 3, adadin da ya kai adadin mutanen da suke zaune a nahiyoyin Turai da Amurka da Afirka da kuma yankin Oceania. A rana ta farko da aka fara aikin wato jiya, adadin fasinjoyin da aka yi jigilar su ta jiragen kasa ya kai sama da miliyan 8 da dubu dari daya, kawo yanzu ana gudanar da aikin yadda ya kamata.

Bikin bazara, bikin gargajiya mafi muhimmanci ne na Sinawa, a don haka yawancin Sinawa su kan koma garuruwansu domin shirye-shiryen shagulgunan bikin, amma wasu kuwa sun fi son fita waje yawon shakatawa yayin bikin bazara, shi ya sa ake fara da aikin jigilar fasinjojin tun daga yanzu, haka kuma za a ci gaba da wannan aikin har tsawon kwanaki 40.

A nan kasar Sin, Sinawa sun fi son shiga jiragen kasa, a saboda haka kamfanin layin dogo na kasar Sin ya fi fama da aiki, mataimakin daraktan sashen kula zirga-zirgar jiragen kasa na babban kamfanin layin dogo na kasar Sin Zhang Caichun ya bayyana cewa, a ranar ta farko da aka fara gudanar da aikin tafiye-tafiyen bikin bazara, an kara yawan zirga-zirgar jiragen kasa har sau 428, a baya kuma, adadinsu ya kai 7638 a fadin kasar, wannan ya sa adadin fasinjojin da aka yi jigilar su ta jiragen kasa ya zarta miliyan 8 da dubu dari daya. Zhang Caichun yana mai cewa, "Bisa yanayin da ake ciki yanzu, an lura cewa, ana gudanar da aikin jigilar fasinjoji yadda ya kamata kuma cikin kwanciyar hankali, misali layin dogo mai saurin tafiya tsakanin biranen Beijing da Shanghai, da layin dogo mai saurin tafiya tsakanin biranen Shanghai da Kunming na lardin Yunnan, da kuma layin dogo mai saurin tafiya tsakanin birnin Xi'an na lardin Shaanxi da birnin Chengdu na lardin Sichuan wanda ya fara aiki ba da dadewa ba, dukkansu suna komai na tafiya lami lafiya, wato jiragen kasan sun tashi kuma sun isa wuraren su a daidai lokacin da aka tsara."

A sakamakon bunkasuwar layin dogo mai saurin tafiya, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin jigilar fasinjoji ta layin dogo, ya zuwa shekarar bara wato 2017 da ta gabata, tsawon layin dogon kasar ya kai kilomita dubu 127, kuma a ciki tsawon layin dogo mai saurin tafiya ya kai kilomita dubu 25, abu mai faranta rai shi ne jiragen kasa wadanda saurin tafiyarsu ya kai kilomita 350 a kowane sati suna karuwa cikin sauri a nan kasar Sin.

Zhang Caichun ya kara da cewa, yayin da bikin Bazara ke kara kusantowa, adadin fasinjojin zai karu matuka, a don haka za a ci gaba da kara samar da jiragen kasa domin biyan bukatunsu, misali kafin bikin, za a kara samar da jiragen kasa har sau 1152, bayan bikin kuma, za a kara 1330, ban da haka kuma, a wasu biranen da suka fi yawan fasinjoji, kamar su Beijing da Guangzhou na lardin Guangdong da Shanghai da Kunming na lardin Yunnan da kuma Harbin na lardin Heilongjiang, za a kara 177 da dare.

A sa'i daya kuma, kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Sin su ma suna kokari matuka yayin tafiye-tafiyen bikin bazara, wato za su kara samar da jiragen sama wadanda za su zirga-zirga dubu 15, tafiya ta kasa wato motoci kuwa, kamfanonin da abin ya shafa za su kara yin amfani da motoci dubu 840 domin jigilar fasinjoji, kazalika, jiragen ruwan da za a yi amfani da su wajen jigilar fasinjoji su ma za su karu har sama da dubu 20.

Shugaban sashen kula da aikin samar da hidima ga fasinjoji na babban kamfanin layin dogo na kasar Sin Li Jianfeng ya bayyana cewa, za su yi kokarin kyautata hidima ga fasinjoji, yana mai cewa, "Yanzu adadin na'urorin tantance fuskokin fasinjoji a tasoshin jiragen kasa a fadin kasar ta Sin ya zarta dubu daya, hakan zai sa fasinjoji su shiga tasoshin cikin sauri kuma cikin tsaro, kana ana samar musu abinci masu dadi da kuma muhimman bayanai."

Yanzu ana yin ruwan sama ko saukar dusar kankara a wurare daban daban a fadin kasar, wannan ya aka gamu da matsaloli yayin da ake gudanar da aikin jigilar fasinjoji, mataimakin daraktan sashen kula da aikin zirga-zirgar jiragen kasa na babban kamfanin layin dogo na kasar Sin Zhang Caichun ya bayyana cewa, a shirye kamfanin layin dogo yake domin magance su, ya ce, "A shirye muke mu magance matsalolin da za mu gamu da su, misali mun shirya na'urorin samar da lantarki da yawansu ya kai 2157 da sauransu a manyan tasoshin jiragen kasa, ko shakka babu za mu daidaita duk kan matsalolin daka iya kunno kai yadda ya kamata"(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China