in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya zai taimakawa Afrika wajen fadada shirin harkokin kudi
2018-02-01 10:24:08 cri
Sashen kula da hukumomi masu zaman kansu na bankin duniya ya sanar cewa zai taimakawa Afrika wajen ba ta damar fadada harkokin kudi ta hanyar fasahar zamani.

Lesley Denyes, manajar shirin cibiyar harkokin Afrika a hukumar kula da hada hadar kudade ta kasa da kasa (IFC) ta bayyana cewa, nahiyar Afrika ita ce mafi karancin shiga harkokin kudi na duniya.

Denyes ta ce za su yi aiki tare da hukumomin kudi masu zaman kansu musamman a fannonin kasuwanci ta yanar gizo da harkokin sadarwa don fadada shirin shigar da Afirka harkokin kudi na kasa da kasa.

Ta ce IFC za ta yi amfani da wannan dama wajen gudanar da binciken kwa-kwaf da kuma gina tsarin amfani da fasahar zamani domin gano adadin kasuwancin hada hadar kudaden da ba'a amfani da su.

A kwanan nan IFC ta kammala wani shirin hada hadar kudi na dala miliyan 37.4 na tsawon shekaru 6 wanda ya shafi ayyuka 23 a kasashen Afrika 13 da nufin fadada hanyoyin da za'a shigar da nahiyar cikin harkokin kudade na duniya.

Denyes ta ce, karkashin wannan shirin, 'yan Afrika miliyan 4.7 ne suka samu damar shiga harkokin hada hadar kudade. A cewarta samun damar shiga harkokin hada hadar kudade babban jigo ne wajen bunkasar tattalin arziki kuma yana iya samar da ci gaba ta fuskar samar da rance kudade. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China